Jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun kai samame gidan dan jaridar nan da ke shiga tsakani wajen sakin fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace a tsakanin Abuja-Kaduna, Tukur Mamu.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, DSS sun samu kayan sojoji, kudaden kasashen waje masu nauyi da kuma wasu takardun ma’amalar kudade a gida da ofisi din Tukur Mamu da ke Kaduna.

Mamu, wanda jami’an tsaro suka kama a Cairo babban birnin Egypt ranar 6 ga wannan watan a kan hanyarsa zuwa Saudi Arebiya domin gudanar da aikin Umara, sun sake shi ya dawo gida.

SaharaReporters, ta ruwaito cewa, jami’an tsaron DSS sun kama Tukur Mamu ne ranar Laraba jin kadan da saukarsa a filin sakar jiragen sama na Malam Aminu da ke Kano shi da matansa biyu da kuma ‘ya’yansa.

DSS sun yi awon gaba da kwamfutoci da wasu takardu masu yawan gaske bayan samamen da suka kai a gida da ofishin mawallafin jaridar Desert Herald.

Kamar yadda mai magana da yawun Hukumar DSS, Peter Afunanya ya bayyana a wani bayani da ya fitar ranar Alhamis, sun samu odar da ta halatta masu binciken da suka gudanar a gida da ofishin Mamu.

Ya ce a binciken da suka gudanar sun gano wasu abubuwa na laifi da suka hada da kudaden kasashe daban-daban masu tarin yawa, kayan sojoji da takardun mu’amala kudade.

Ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da Mamu a gaban kotu.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *