Daga Shu’aibu ibrahim Gusau

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Kuma dantakarar kujeran sanata ta Yamma, Abdul’aziz Yari Abubakar ya yi kira ga ‘Ya’yan jam’iyyar APC a jihar da su Fito kwansu da kwarkwatansu don karbar katin zabe na dindindin (PVC) a yankunansu.

Ya Yi wannan kiran ne a wajen kaddamar da kwamitocin yakin neman zaben gwamnan jihar, Bello Muhammad matawallen maradun na jam’iyyar APC, wadanda suka Fito daga kananan hukumomi 14 dake fadin jihar, shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a jihar a zaben 2023 mai zuwa, Wanda shine Tsohon Gwamnan Abdul’aziz Yari ya ce ‘Yayan jam’iyyar su kasance suna da katunan zabe.

Yari ya bayyana PVC a matsayin mai matukar muhimmanci wajen kada kuri’a, inda ya ce idan ba haka ba, ba za a bari kowa ya yi amfani da ‘yancinsa na tsarin mulki a lokacin babban zabe ba, ya Kara da cewa “Ina amfani da wannan damar domin yin kira ga daukacin kungiyoyin matasa da mata na jam’iyyar APC da su hada kai su karbi wannan Kati na PVC.

Yari yace “Duk masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar su fara kamfen na tattara PVC a yankunansu, ya Kara da cewa “Ya kamata mu yi amfani da damar mu kuma mu hada kai domin samun nasara a babban zaben 2023 a jihar Zamfara da kasa Baki daya” in ji shi.

Yari ya ce za a fara yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC a karamar hukumar Kaura Namoda, a ranar 26 ga watan Disamba. “Ina mai tabbatar muku da cewa idan aka fara yakin neman zaben gwamnan APC, za ta nuna irin karfin da jam’iyyar APC ke da shi.

Gwamna Bello Muhammad Matawalle a nasa jawabin a wajan taron ya yabawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da ‘ya’yan jam’iyyar da magoya bayansa bisa kokarinsu na ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a jihar, musamman ya yabawa Yari da ’yan majalisar yakin neman zabensa kan yadda jam’iyyar ta yi tasiri da karfi a jihar. in ji Matawalle.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *