Daga Bello Hamza

Da safiyar yau Laraba 17 ga watan Mayun 2023 daidai da 27 ga Shawwal 1444 aka raɗa sunan ɗiyar da aka haifawa Editanmu, Ammar Muhammad Rajab.

An yi zanen sunan ne da misalin ƙarfe 7 na safe a ƙofar gidan mahaifinsa dake Anguwar Mai Gwado Sabon Gari Zariya dake jihar Kaduna.

Al’umma da dama ne suka taru domin shaida raɗin sunan da Limamai da Malamai suka jagoranta.

An sanya wa jaririyar da aka haifawa Editan namu da sunan Aaliyah.

Editan na mu ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa; “Ɗiya ta ci sunan Sayyida Fatima, an sanya mata suna Aaliyah da safiyar yau Laraba. Za mu riƙa kiranta da Aaliyah. Muna addu’ar Allah ya yi wa rayuwarta albarka”, in ji shi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa; “Mungode sosai da adduo’inku, da masu turo sakonnin taya murna da kiran waya da ake ta ta yi tun daga ranar haihuwar har zuwa yau da aka yi zanen suna.

“Sakon godiya sosai ga wadanda suka yi tattaki har zuwa kofar gidan mahaifinmu suka shaida wannan zanen sunan. Da masu turo sakonnin ta shafukan Facebook da WhatsApp, Allah ya girmama ladanku. Mungode sosai”, ya ƙarƙare.

A madadin shugaban kamfanin jarifdar Idon Mikiya, Alhaji Mansur Aliyu, muna taya Ammar murna tare da addu’ar Allah ya raya mana yarinyar a bisa tafarkin addinin musulunci.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *