Ragowar fasinjojin da aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi kira ga manyan kasashen duniya da su taimaka su shiga tsakani a kan halin da suke ciki da kuma ganin an ceto su daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.

Idan za a iya tunawa, ‘yan ta’adda sun kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna hari a daren ranar Litinin 28 ga watan Maris, 2022, inda fasinjoji tara suka mutu, sannan suka yi awon gaba da wasu da dama yayin da aka ceto wasu da dama da raunuka.

Mamu wanda ya jagoranci yin sulhu har aka sako mutane 18 daga cikin fasinjojin rukuni na biyu. Sun saki mutane 11 a ranar 11 ga Yuni, 2022, sai kuma suka sake sakin wani rukuni na fasinjojin bakwai a ranar 9 ga Yuli, 2022.

‘Yan ta’addan sun yi barazanar kashe sauran wadanda ke hannunsu, matukar gwamnatin tarayya ba ta biya musu bukatunsu ba, ciki har da bukatar sakin mayakansu da ake tsare da wadanda aka samu da laifi da kuma wadanda ke jiran hukuncin shari’a.

Daga bisani ‘yan ta’addan na Boko-Haram sun kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja, inda suka saki daruruwan fursunonin da suka hada da wasu 69 daga cikinsu da ke fuskantar tuhumar ta’addanci.

Da yake mayar da martani kan harin, Mamu, ya sanar da janye wa daga tattaunawar neman sakin fasinjojin jirgin da aka sace, inda ya bayyana rashin kulawa daga gwamnatin tarayya ke nunawa da kuma barazana ga rayuwarsa da yake fuskanta.

Ya kuma zargi gwamnatin tarayya gaza yin katabus game da bayanan sirri kan yiwuwar harin na gidan yarin Kuje.

A wani sabon faifan bidiyo da ‘yan ta’addan suka fitar a ranar Asabar, wanda LEADERSHIP ta samu, an ga yadda ‘yan ta’addan ke yi wa wadanda aka yi garkuwa da su bulala, wadanda suka hada da manya maza da mata da kananan yara.

A cikin bidiyon mai tsawon mintuna 10.51, ‘yan ta’addan sun yi barazanar yin garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai tare da kashe su.

‘Yan ta’addan sun kuma sha alwashin cewa za su ruguza kasar nan, su kashe sauran fasinjojin da ke hannunsu sannan su sayar da sauran.

Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya yi barazanar cewa idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar mahauta.

“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Nijeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane a nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnoninku za su zo gabanmu. Wadannan da kuke gani a nan za mu rike wasu a matsayin bayi, mu sayar da su kamar yadda Imaminmu ya fada muku a baya,” in ji shi.

Bayan ‘yan ta’addan sun yi magana, wasu daga cikin fasinjojin da aka sace sun roki gwamnatin tarayya da manyan kasashen duniya irin su; Faransa, Amurka, Ingila da sauransu da su kawo musu dauki.

Sun koka da halin da suke ciki tare da zargin gwamnati da rashin nuna kulawa, inda suka kara da cewa wadanda suka sace su sun fi mutunta su fiye da gwamnatin Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *