Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sabon Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya Koka da yadda tsohon gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje ya bar masa bashin da yakai sama da Naira Biliyan 241 . Wanann abun da tsohuwar gwamnati ta yi mana abun takaici ne na bar masa bashin da yakai Sama da Naira Biliyan 241, a Ina za mu samu wadannan kudaden har mu biya”. Inji Abba Kabir

Sabon gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya karɓi ragamar mulkin jihar Kano a Gidan gwamnatin Kano.

Abba Kabir Yusuf ya bada tabbacin zai duba yadda gwamnatin tada gabata ta gudanar da mulkin da kuma daukar matakan da suka dace.

” Na zaci tsohon gwamna Ganduje zai tsaya da kansa ya mika mulki kamar tadda aka Saba a nan kano, a Shekarar 1999 Kwankwaso ya mila mulki ga Kwankwaso, Kwankwaso kuma ya mika mulki ga Shekarau a 2003 , haka kuma Shekarau ya mikawa Kwankwaso mulki a Shekarar 2011, shi ma Kwankwaso ya mikawa Ganduje Kwankwaso mulkin a Shekarar 2015 , amma kuma ni Mai yasa ba zai tsaya ya mikamin mulki ba sai dai ya sa wakili ? “. Inji Abba Gida-gida

Engr. Abba Kabir ya baiwa al’ummar jihar kano tabbacin gwamnatin sa zata yi duk mai yiyuwa wajen ganin bai basu Kunya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *