Daga Ibrahim Muhammad Kano

Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta bayar da tallafi ga karin ‘yan Najeriya da aka dawo da su gida Nigeria sakamakon rikicin Sudan.Mutune 125 na baya-bayan nan da suka hada da nakasassu da dama da Kamfanin Jirgin Sama na Tarco ya yi jigilar su zuwa Abuja a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni, kowannensu ya rabauta da Naira 100,000 daga gidauniyar Aliko Dangote.

Gidauniyar ta sake bada gudunmawar ne don samun saukin dawo da ‘yan kasar da aka kwaso daga Sudan kuma daga cikinsu akwai tsofaffi, nakasassu, matasa, mata da yara.

Wasu mutane biyu ‘yan shekara 70 da suka yi niyyar tafiya ibadar umrah sun fada cikin rikicin lokacin da suka ya da zango a kartum, Inda kuma guzirunsu ya kare.

‘Yan Nijeriya da dama ne suka yi asarar sana’o’insu daban-daban sakamakon yakin, sana’o’in da suka hada da fata, dinki, yin takalmi, saye da sayar da dai sauransu

Wani dattijo mai suna Muhammad Saidu Ahmed ya ce ya Sudan ba ko kwabo ba’, yanzu ina da Naira 100,000a

Wata mata mai shekaru 80, ta ce yawancin iyalanta sun yi nasarar tserewa rikicin, sun shiga tashin hankali sakamakon tashin bama-bamai wanda hakan yasa suka rika fama da yunwa, sannan sun yi asarar gidajensu da wasu daga cikin yan uwansu.

Sun godewa gidauniyar Aliko Dangote, ADF, bisa wannan taimakon, wanda suka bayyana a matsayin wanda ya zo musu basu zata ba, Kuma zai taimaka musu sosai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *