Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya ba da  umurnin  fitar da Kudi Naira Biliyan 2,566,580,098.35 (Biliyan biyu da dari biyar da sittin da shida da dari biyar da tamanin da dari biyar da tamanin da takwas da tasa’in da takwas da kobo talatin da biyar domin biyan kudin hutun shekaru biyu na shekarar 2021 da 2022 na Ma’aikatan Jihar,  Kananan Hukumomi da Hukumar Ilimi ta Kananan Hukumomi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da Kwamishinan kudi, Ibrahim Muhammad Augie, aka kuma rabawa  manema labarai a Birnin Kebbi ta hannun Mai ba Gwamna shawara kan harakoki yada labaru Yahaya sarki.

A cewar sanarwar, gwamnatin Jihar Kebbi a karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta saba biyan bukatun da ya rataya a wuyanta na ma’aikatanta  da masu ritaya.

Hakazalika, Sanarwar ta ci gaba da cewa, Jihar Kebbi  na daga cikin jiga-jigan jahohin da suka fi kowa samun walwala da ci gaban ma’aikata. Dukkan albashi, fansho, gratuity, kudaden  hutu, karin girma, ci gaba da horarwa gwamnati  na biya kankari da Kuma  kula da su akai-akai tun daga shekarar 2015 zuwa yau.

Kwamishinan ya yi kira ga ma’aikata a Jihar da su  kara yaba wa kokarin gwamnati ta yadda a kullum suke yin iya kokarinsu wajen jajircewa, amana da aiki tukuru don taimakawa gwamnati wajen cimma dukkanin kyawawan tsare-tsare da ta ke bi wajen daukaka ci gaban Jihar baki daya zuwa wani matsayi mai girma,  inji Kwamishinan ma’aikatar Kudi ta Jihar, Ibrahim Muhammad Augie.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *