Daga Ibrahim Muhammad Kano

Anyi kira ga Gwamnatin Kano  da masu hali da sauran al’umma akan su kara kaimi wajen  taimakawa cigaban makarantun Islamiyya dake lungu da sakon jihar.

Babban mai taimakawa Gwamnan jihar Kano na musamman akan.Kasuwannin jihar Kano na harkar yanar gizo guda 174 .”Public Beneitization on E-trade and marketing strategies.Tsohon dan takarar Gwamnan Kano kuma   shugaban kungiyar yan takarar Gwamna a kananan jam’iyyu da suka janyewa Ganduje a  2019.Hon.Ghali Auwalu Goro Kofar Mata ne,ya yi kiran a yayin taron saukar karatun Kur’ani na dalibai 157 na makarantar.Asharatul mubasshirul bil-jannati

Yace yakamata mutane su zama masu taimako,saboda yanzu anzo wani hali da mutanenda basuda hali sai dai suje kafafen labarai suna neman taimako.

Ya yi nuni da cewa Kano garine na kasuwanci,na masu arziki,idan ana taimakon juna za’a rage talauci,sai aga kamar babu shi.Zai zama idan marashi ya tashi,zai aurar da yar’sa yazo neman taimako,inda halinda za’ayi mata kayan daki ma ayi mata,in kuma kanada hali zaka auri yar talaka da ba shida halin yi mata kaya,kayi mata,kace kai baka bukatar komai  ka taimakeshi

Ya yi kira ga al’umma su rika amfani da damarda Allah ya basu wajen taimakon mutane da basuda hali.Makarantun Islamiyya sunada bukatar taimakon Gwamnati,kuma a matsayinsa na babban mai taimakawa Gwamna Ganduje duk da ba bangaren ofishinsa bane, zai nemi a kawo musu dauki ta yiwa Gwamna magana kai tsaye a duba makarantun Islamiyya a bada   gudummuwa a  tallafa musu,donin  wasu sunada fili basuda yanda zasu gina,wasu an fara ginin  ba halin kammalawa a waje da sorayen gidaje suka zama komai ruwa komai sanyi.Saboda irin wannan kishi shi  yasa shima ya bada tallafi  na N50,000 duk da ba yawa, amma da yardar Allah  Gwamnati zata shigo irin wannan al’amari.

Hon.Ghali Kofar Mata yace shi dama Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje  mutumne mai kishin cigaban addini, shi yasa ake kiransa “khadimul Islam” Dan ya yi shura wajen taimakawa addini a bangaren Musuluntar da Maguzawa da aljihunsa, bana Gwamnati ba, yanada Gidauniyar  wacce take yawo lungu da sako samada da shekara 30 tun yana ma’aikacin Gwamnati,bai san ma zai shiga siyasa ya tsaya takara ya zama Gwamna ba, yake musuluntarda maguzawa ya Gina musu masallaci asa musu malamai su koyar dasu addini a gina musu makaranta.

Babban mai taimakawa Gwamna Ganduje akan kasuwannin yanar. Gizon.Hon.Ghali Auwalu Goro Kofar Mata yace Gwamna Ganduje na gina masallatai na Juma’a da taimako ga makarantu,dan haka zai bashi shawara, suma makarantun Islamiyya a shigar dasu cikin Gidauniyarsa kari akan yanda ake daukar nauyinsu a  musabakar.

Pic.
Hon.Ghali Auwalu Goro Kofar Mata. .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *