Daga Ibrahim Muhammad Kano

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da karin nadin mukamai guda biyar daban-daban a jihar.

Wadanda aka nada sune kamar sune.Injiniya Garba Ahmed Bichi

Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano

da Dokta . Rahila Mukhtar

Babban Sakatariyar Hukumar Kula da Gudunmawar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano.

Karin nade-naden su hada da Hassan Baba Danbaffa a matsayin

Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano (KARMA).

Sai Mazayyani Ibrahim Yakubu

Manajan Daraktan Hukumar Tsare-Tsare da Cigaban Birane ta Jihar Kano (KNUPDA).

Da kuma Abdulkadir Abdussalam

Akanta Janar na Jihar Kano

Nan ba da jimawa ba za a sanar da bikin rantsar da wadanda aka nada domin ba su damar sauke nauyin da aka dora musu nan take.

Wannan kushe ne cikin takardar da Sanusi Bature Dawakin Tofa sakataren yada labaran Gwamnan Kano ya sa hannu aka rabawa manema labarai ciki da jaridar idon mikiya/factual.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *