Daga Ibrahim Muhammad Kano

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba da tabbacin gwamnatinsa na shirin sake fasalin kasuwannin Kano ta hanyar daukar kowa da kowa.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin samar da sahihin wakilci na ‘yan kasuwa a kwamishinonin sa, inda ya kara da cewa kwamishina zai fito daga cikinsu da sauran mukamai da za su baiwa al’umma kyakkyawan wakilci.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnan Hisham Habib, ta ce gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da ‘yan kasuwa a lokacin da ya karbi bakuncinsu a gidan gwamnati.

A cewar sanarwar gwamnatin mai ci za ta bunkasa harkokin kasuwanci a jihar tare da tabbatar wa yan kasuwar kudirinsa na tallafawa hanyoyin kasuwanci na zamani musamman ta fasahar zamani.

Gwamnan ya kuma shaidawa ‘yan kasuwar shirin sake fasalin kasuwannin Kano tare da tafiya da kowa.

Ya ce gwamnati za ta kuma rage cunkoso a birnin ta hanyar bude sabbin wuraren kasuwanci, ya kuma bukaci matasan ‘yan kasuwa da su yi amfani da wannan damar dan bunkasa cigaban Kano..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *