Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tsohon dan takarar majalisar jiha a karamar hukumar Gwale kuma mataimakin darakta na yada manufar matasa na Kano ta tsakiya na takatar  shugabancin kasa na Kwankwaso da Injiniya AbbaذKabir Yusuf da sanata Rufa’i Sani Hanga.Hon Jamilu Tijjani Yamadawa ya bayyana  nasarar Injiniya Abba Kabir Yusuf daga Allah take,wanda ya samu  bisa aiki da akayi tukuru  ya haifar da sakamako mai kyau.

Ya ce irin yanayin da al’ummar Kano suka tsinci kansu, dama basa tunanin akwai wani talaka da zai sake yarda ya zabi mutanenda suka jefa rayuwarsu a cikin bala’i da ake ciki yanzu.

Ya ce tunda yake, bai ta ba jin inda aka ce an yi wa Gwamnati magudi ba,ko ace ta yi wa kanta zanga-zanga ba, ko kuma ta yiwa talakawan gari, wannan duk wani abune da yake nuna shure-shure ne da baya hana mutuwa saboda  sun je kasa shine suke fuffukar an musu magimudin zabe

Hon.Yamadawa ya  kara da cewa da yardar Allah zabe ma da za’a sake na matakin wasu yan majalisu da za’a karasa gaba daya NNPP ce za ta lashe.

Hon.Jamilu  ya ce ba suda wani tanadi na daukar fansa a gwamnatin NNPP  sai dai, illa duk wani abu da aka taras akan ka’ida ba za su ta ba shi ba,amma duk wanda ba akan ka’ida ta doka aka yi ba,kuma zai cutar da talaka to za’ayi masa duba na tsanaki, saboda wannan Gwamnati ce ta talaka dan talaka

Ya jinjina wa  al’ummar kasar nan musamman mutanen jihar Kano da  yi musu godiya akan yanda suka fito su ka zabi Abba a matsayin Gwamna, tareda yabawa dukkan hukumomi na tsaro da hukumar zabe ta kasa bisa tabbatarda yin zabe sahihi ta tsayawa da yin aiki tukuru ba tare da son rai.

Hon.Jamilu Tijjani ya ce sunada yakinin a Gwamnatin Abba Kabir sai al’,ummar Kano sun ji dadi,domin  za’a zo da gyara, duk wani hakkin talaka, sai an mallaka masa dan kyautata rayuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *