A ranar Alhamis ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta kaddamar da sabon tsarin karatarwa da aka yi wa lakabi da “Nigeria Learning Passport’’ don bunkasa ilimi a matakin Firamare, Sakandare da kuma al’ummar jihar gaba daya.

A yayin kaddamar da shirin a garin Kaduna, Kwamishiniyar Ilimi, Hajiya Halima Lawal, ta ce, an yi fito da sabon tsarin ne don samar da ingantacciyar ilimi kamar yadda ake gudanarwa a sassan duniya.

An samar da shirin ne don kara inganta harkar ilimi ga yara ‘yan firamare da sakandire a sassan jihar.

Shirin dai ya samu albarkacin ma’aikatar ilimi ta tarayya an kuma samar dashi ne don kulle ratar da ake samu a tsakanin al’umma wajen samun ingantacen ilimi.

A jawabinsa Msta Francis Elisha, wanda shi ne wakilin majalisar dinkin duniya na UNICEF ya ce,annobar Korona ce ta tilasta neman hanyoyin cigaba da karantar da yara a lokacin da sake fuskantar kulle, ya kuma yi alkawarin tallafa wa shirin musamman ganin muhimancisa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *