Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe Hanifa Abubakar, dalibar makarantarsa.

Kotun, ta kuma samu abokinsa, Hashim Isiyaku wanda shi ne ya binne Hanifa a cikin makarantar, bayan an hada baki wajen aikata laifin da shi kuma shi ma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya da daurin shekara biyu.

Sai budurwar Abdulmalik Tanko, Fatima Jibrin, wadda aka hada baki da ita wajen yin garkuwa da Hanifa tun farko, ita kotun ta same ta da laifin yunkurin yin garkuwa da mutum kuma ta yanke mata hukuncin shekara biyu.

Alkalin kotun, Sulaiman Na’Abba, ya bayyana cewa bayan hujjojin da lauyoyin kowanne bangare suka bayar, kotu ta samu Abdulmalik Tanko da Hashim Isiyaku da laifin garkuwa da Hanifa, da Kuma bata guba (shinkafar bera) ta mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *