Daga Waziri Mahdi Isa

A ranar Lahadi, 21 ga watan Aprilu ne Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta bada shaidar girmamawa ga wasu manyan malaman addinin musulunci na Najeriya da Marigayi Sarkin Kano Alh Ado Bayero saboda hidimarsu ga Al-Qur’ani mai girma.

Manyan malaman sun haɗa da fitaccen malamin ɗariƙar Tijjaniyya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi; fitaccen malamin ɗariƙar Qadiriyyah, marigayi Sheikh Nasiru Kabara; da kuma fitaccen malamin ƙungiyar Izala, marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam.

Wakilin ƴan uwa na harkar musuluncin na jihar Kano, Sheikh Dr. Sunusi Abdulqadir ne ya miƙa shaidar girmamawar ga wadannan manyan mutane bisa hidimarsu ga Al-Qur’ani da ma’abotansa.

Wadannan mutane sun samu wannan shaidar girmamawar ne a ‘Ranar Mahaddata’ karo na 12 da ƴaƴan harkar musuluncin suka saba gabatarwa a birnin Kano.

A wannan karon, an yaye mahaddatan Al’Qur’ani kimanin mutum 200, maza da mata.

Bayan gwada haddar mahaddatan da kuma yi musu darasu daga gwanayen Al-Qur’ani, a ƙarshe an miƙa musu shahadar haddace Al-Qur’ani mai girma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *