Daga Ibrahim Muhammad Kano

Hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Kano ta yi taron nunawa maniyyata yanda ake aikin hajji a aikace Wannan na zuwa ne bayan kwashe watanni ana yi musu bita a cibiyoyi dake kananan hukumomi 44 na jihar.

Taron nuna yanda ake gudanar da aikin hajjin ya gudana ne a sansanun Alhazai na jihar Kano da ya sami halartar dinbin maniyyatan.
Babban sakataren Hukumar Alhazai na jihar Kano Ambasada Abba Danbatta ya ce ranar Uku ga watan gobe ne.Maniyyatan na jihar Kano zasu soma tashi zuwa kasa mai tsarki.

Ya ce ya godewa Gwamnan jihar Kano bisa dama da ya bashi na bashi dama wajen bada gudummuwa kusan shekara Shida a hukumar Alhazai.

A madadin mai girma Gwamnan Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya umurceshi ya yi kira ga maniyyatan su kasance masu bin doka da oda a kasa mai tsarki da na wannan kasa.

Ambasada Danbatta ya godewa dukkan masu ruwa da tsaki a hukumar jin dadin Alhazai kan goyon baya da suka bashi na cimma nasararin gudanarda aikin hajji.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *