Daga Bello Hamza

Hukumarkula da iyakokin ruwan kasar ta kaddamar da manhajar zamani ga ma’aikatan iyakokin ruwan kasar don saukaka da kuma inganta ayyukan su.

Mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ne ya bayyana haka a sanarwar da ya rabawa manema labarai a birnin ikko.

Sanarwar ta ce Shugaban hukumar, Dr Bashir Yusuf Jamoh ya bayyana kaddamar da manhajar a matsayin wata hanyar zamanatar da ayyukan ma’aikatan iyakokin ruwan kasar nan, inda yayi nuni da cewa hakan zai taimaka matuqa kuma ya kasance wani kundi na adana bayanan ma’aikatan iyakokin ruwan kasar nan.

Shugaban hukumar wanda Engineer Victor Ochei ya wakilta yace manhajar zata kuma taimakawa ma’aikatan wajen yin tsimi da kuma inganta ayyukan su.

Ana kuma sa ran manhajar ta zamani zata saukaka samar da shaidar katin aiki na zamani ga ma’aikatan.

Dr Bashir Yusuf Jamoh ya kuma jaddada aniyar hukumar wajen tabbatar da cewa ma’aikatan hukumar suna samun horo akai-akai don bangaren iyakokin ruwan kasar nan tayi gogayya da sauran takwarorin ta na duniya.

A nashi tsokacin, Shugaban kungiyar ma’aikatan iyakokin ruwan kasar nan, Comrade Adewale Adeyanju bayyana farin cikin shi yayi dangane da samar da wannan manhaja ta zamani, sannan ya yabawa hukumar NIMASA bisa kokarin ta wajen inganta ayyukan bangaren iyakokin ruwan kasar nan da ma’aikatanta ta hanyar basu horo yanda ya kamata.

Taron ya samu halartar wakilan manyan masu ruwa da tsaki a bangaren harkar iyakokin ruwa, da na masu dakon jiragen ruwa, da na masu fito na kasa, da na masu kula da shige da fice na kasa, da na hukumar hana fasa kwauri na kasa, sai kuma wakilin kwamishinan ‘yan sanda na tashar ruwan Apapa da sauran manyan baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *