Daga Bello Hamza

ukumargudanarwa ta NIMASA ta gana da Shugabannin bankunan Ja’iz, UBA, bankin Union, bankin Zenith da Polaris wadanda sune bankunan da gwamnatin tarayya ta amince za su bada tallafi ga mamallaka jiragen ruwa.

Da yake jawabi bayan ganawar sirri da bankunan, Shugaban hukumar, Dr Bashir Yusuf Jamoh yayi nuni da cewa ganawar wani mataki ne wajen aiwatar da umarnin na Shugaban kasa kamar yanda Ministan harkokin sufuri, Injiniya Mu’azu Jaji sambo a bara.

Shugaban hukumar ya kara da cewa manufar ganawar itace don samun fahimta tsakanin bankunan da wadanda za su amfana da wannan tallafi don inganta tattalin arzikin kasa.

Dr Bashir Jamoh yayi bayanin cewa ganawar ya zama wajibi saboda bankuna ne ke da kwarewa wajen yanda za a raba tallafin ba tare da wani tsaiko ba, inda ake sa ran bankunan su fito da tsare-tsaren da za a bi don samun wannan tallafi.

A nasu bangaren, wadanda za su amfana da wannan tallafin sun bada tabbacin amfani da tallafin don cimma manufar da aka sanya a gaba.

A nashi tsokacin, Shugaban bankin Ja’iz, Dr Sirajo Salis, wanda yayi tsokacin a madadin sauran shugabannin bankunan, ya sha alwashin tabbatar da an raba wadannan tallafin akan lokacin, inda ya bukaci wadanda za su amfana da su kiyaye dokokin dake kunshe wajen samun tallafin gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *