Daga Bello Hamza

A kokarin ta wajen inganta ayyukan ta daidai da tsarin manufofin da aka kafa ta, hukumar kula da iyakokin ruwan kasar ta shirya taron bitar karawa juna sani na yini uku ga manyan jami’an ta.

A sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai a birnin Ikko, yace Shugaban hukumar, Dr Bashir Yusuf Jamoh yayi bayanin cewa ganawa da masu ruwa da tsaki na cikin gida wani ginshiki ne na tabbatar da nasarar aiwatar da manufar samar da tsaro a iyakokin ruwan kasar nan da kuma inganta zirga-zirgar jiragen ruwa.

Dr Bashir Jamoh yace a kokarin cimma burin manufofin hukumar, hadin gwiwa daga dukkanin masu ruwa da tsaki ya zama wajibi don jawo hankulan masu zuba hannayen jari a bangaren iyakokin ruwan kasar nan.

Yayi nuni da cewa hukumar NIMASA ta maida hankali ne wajen aiwatar da manufar gwamnatin tarayya wajen jawo hankulan masu zuba hannayen jari, da kuma inganta hazakar ma’aikatan ta don yin gogayya da takwarorin su a fadin duniya.

A maqalar da ya gabatar, Darakta Janar na kwamitin tattalin arziki na kasa, Mr Laoye Jaiyeolawho ya lura da cewa bangaren iyakokin ruwan kasar nan na da muhimmiyar gudunmawar da za ta iya badawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

Ya kuma bukaci hukumar gudanarwar NIMASA da suyi dukkanin mai yiwuwa wajen ciyar da bangaren gaba daidai da cigaba na zamani.

Yayi nuni da cewa bisa la’akari da yakin Ukraine da Rasha da kuma sauyin da aka samu a duniya sakamakon barkewar cutar kwaronabairos, yin amfani da kimiyyar zamani zai taimakawa Nijeriya wajen samar da jagoranci a bangaren iyakokin ruwa.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar NIMASA karkashin jagorancin Dr Bashir Yusuf Jamoh tana cigaba da shirya bitoci ga bangarori daban-daban na hukumar don samun nasarar aiwatar da manufofin kafa hukumar.

Shi dai wannan taron na bitar da aka shiryawa manyan jami’an hukumar na bana an tsara shi ne don cimma manufofin hukumar na gajere, matsakaici da dogon zango na shekaru takwas masu zuwa don inganta ayyukan hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *