Daga Ibrahim Muhammad Kano

Babban rijistara na hukumar yiwa kamfanoni rijusta na kasa.Alhaji Garba Abubakar ya bayyana cewa sun gudanarda taronne a jihar Kano na wuni Daya dan wayar dakan abokan huldarsu akan sabon tsari da suka kawo na sabon manhaja da suka fito dashi na gano gaskiyar su wanene masu ainihin kamanfani.

Da kuma wanda idan kamfani ko kungiya zata kawo bayananta na karshen shekara da kudadenda ta samu da abubuwa da masu binciken kudinsu sukayi akwai sabon tsari na kawowa da sukayi da ba sai sun kawo hoton takarda sun turo musu ba.

Yace zasu shigarda bayananne ta manhajan zai rike duk lokacinda suke neman bayanin zasu iya shigarda sunan kamfani su biya a basu bayanin haka ake a wasu qasashen Duniya wannan wani matakine na sauqaqawa mutane.

Babban rijistaran na hukumar yiwa kamfanoni da kungiyoyi rijista na kasa Alhaji Garba Abubakar ya kara da cewa a baya akan samu bada bayanai mabambanta in sunje wasu hukumomin sai su bayar daban-daban sai a sami kamfani daya da bayanai hudu da bambamci,yanzu ta wannan sabon shafin hukumomi na Gwamnati zasu sami damar ganin abinda aka shigar, nan gaba kamfani bazai bada bayanai daban-daban ba idan sukayi karya za’a gano nan da nan cikin sauki.

Yace shi yasa suka shirya taron wayar dakan masu hulda dasu da sauran jama’a su gane tsarin da sanin yanda zasu shigarda bayanin da kuma yanda in suna neman bayanin su san yanda zasu nema.

Garba Abubakar ya yi nuni da cewa jihar Kano wuri ne mai muhimmanci a wajensu,saboda cibiyar kasuwanci ne na Arewa akwai dubban yan kasuwa da kamfanoni da kwararrun masana na ilimi a fannoni da dama.Kuma sun gudanarda irin makamancin irin taron a Legas da Abuja sai wanda suke a Jihar Kano.

Pic.Babban Rijistara na hukumar yiwa kamfanoni Rijista na kasa.Alhaji Garba Abubakar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *