Daga Ibrahim Muhammad

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce idan Allah ya bashi nasara acikin sheƙarar farko da zai shiga ofishi zai gyara hanyar Mubi Zuwa Yola, sannan  zai kai yan Mubi su samo ilimi mai zurfi, a kasashen Turai.
Ya fadin hakan ne a lokacin da ya ziyarci fadar mai marataba Sarkin Mubi Dakta Alh, Isa  Ahmadu, Kwankwaso ya kuma kaddamar da sabon ofishin jam’iyyar NNPP da ke shiyar Adamawa ta Arewa.
Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya samu rakiyar injiniya Buba Galadima da dan takarar kujerar majalisar dattawa Dakta Abdullahi Belel, da dan takarar neman kujerar majalisar dokokin Mubi ta Arewa Barista Giddado Ladde da Hon Hamza Zubairu n da ke Unguwar Lokuwa.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *