Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An rantsar da Injiniya Bashir Qaraye a matsayin sabon shugaban jam’iyyar ADP na jihar Kano.

Da yake jawabi bayan tabbatar dashi a matsayin shugaban jam’iyya Injiniya Bashir Qaraye yace ADP jam’iiyyace  mai son zaman lafiya wacce zata tabbatarda ingantacciyar siyasar Damakwaraxiyya ta gaskiya da ba ruwanta da siyasar kabilanci,vangaranci ko addini

Yace qara da cewa jam’iyyace mai rajin gani hadin kai a Nijeriya Dan samun zaman lafiya da kyakkyawan tsaro da cigaban kasa wannan tasa jama’a keta shigowa cikinta run daga shigowar Sha’aban Sharada wannan kuma alamune na nasara.

Injiniya Bashir karaye ya yi kira ga yan jam’iyyar ta ADP su basu cikakkiyar had in kai da goyon baya domin cigaba da bunkasarta.

An sami sauyi a shugabancin jam’iyyar ADP na jihar Kano ne dai a sakamakon zama dan takarar mataimakin Gwamna da tsohon shugaban jam’iyyar Rabiu Bako ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *