Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyana baiwa jigo a siyasar Makoda da Danbatta Hon.Ali Haruna Makoda kwamishinan ruwa na jihar Kano da cewa an bashi ma’aikata muhimmiya domin babu wata Gwamnatin da zata zo bata kalli harkar ruwa ba saboda amfaninsa a Duniya.

 

Dokta Saleh Musa Wailare ne ya bayyana hakan ga yan jarida a ya yinda ya kai ziyarar taya murna ga kwamishinan a ofishinsa.

 

Ya ce yanda aka kalli Ali Haruna Makoda aka bashi ma’aikatar ruwa an san zai hidimtawa jama’a ya amfane su ya kuma amfanarda kowa kuma suna kyautata zaton yanda harkar samar da ruwa ta lalace a Kano zai kawo gyara dan mutum ne mai tunani da hangen nesa da hankali da kamala.

 

Ya ce ko a lokacin da ya yi shugaban karamar hukuma a Makoda ya taimakawa mutane ta bangarori da yawa, ta bangaren ruwa anyi rijiyoyin burtsatse dan haka suna kyautata zaton wannan ma’aikata zata inganta zata sami sababbin abubuwa na zamani da zasu sa Kano ta zama ta wadata da ruwa da yardar Allah.

 

Ya yi addu’ar Allah zai riko da hannayensa da amfani da irin kyawawan shawarwari da zai samu daga abokan aiki dasu magoya baya da zasu bashi dan a kauda matsalar ruwa a kano ta dawo sabuwa fil.

 

Dokta Wailare ya ce Gwamnatin jihar Kano sabuwa ta Abba gida-gida lokacin da akayi takara an fita an nemi jama’a anyi musu alkawarurruka da dama dan haka suna addu’a. Allah ya yi riko da hannayen Gwamnan da jagororinsu da suke tare dashi da jagoransu injiniya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

 

Wailare ya ce yanzu gashi wannan alkawarurruka da akayi kafin zabe yanzu da soma gwamnatin an soma aiwatar dasu, mutane na jin dadin hakan suna fata zai cigaba da sauke nauyin al’ummar Kano.

Dokta Saleh Musa Wailare ya yi kira ga al’ummar Danbatta da makoda da jihar Kano gaba daya su kalli wannan gwamnatin su san cewa cigaban al’umma ta sa a gaba,mai tausayi da gaskiya da rikon amana wanda talaka zai kalli manufofinta ya ji dadi.Dan haka su bata hadin-kai da goyon baya da yi mata kyakkyawan addu’a na cimma nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *