Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi (FUBK) a taronta na 23 da ta gudanar ta amince da karin girma ga ma’aikatan ilimi guda uku zuwa matakin Farfesa da uku zuwa Associate Professor (Readers).

Majalisar ta amince da shawarwarin masu tantancewa na waje da na kwamitin kula da nadawa da kara girma (SSAPC) don aiwatar da karin girma.

Sabbin Farfesoshi da aka karawa matsayi sun hada da Dokta Aliyu Abdullahi Turaki (Molecular Biology), Dokta Abbas Yusuf Bazata (Food and Industrial Microbiology) da Dokta Abdulaziz Shehu na sashen bunkasa tattalin arziki (Economics).

Farfesa Aliyu Turaki shi ne Daraktan Tsare-tsaren Ilimi kuma Mataimakin Darakta, Makarantar Nazarin Digiri na gaba; Farfesa Abbas Bazata shi ne Darakta, Cibiyar Bincike ta Biosciences (Centre of Excellence) kuma Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’in Nijeriya (ASUU), yayin da Farfesa Abdulaziz Shehu kwararren masanin tattalin arziki ne kuma malami a sashen tattalin arziki(Economic).

Abokan huldar Farfesa (Masu karatu) a daya bangaren, Dokta . Muhammad Muazu Yusuf na bunkasa tattalin arziki (Development Economics), Dokta . Victoria Ogunnike Faleke (Pragmatics and Multimodal) da kuma Dokta . Yahaya Tajudeen (Genetics and Toxicology).

Haka kuma majalisar gudanarwar ta kara da cewa” Karin girman ya fara aiki ne tun daga watan Janairu, 2022. Don haka majalisar ta umarci sabbin Malamai da masu karatu da su ci gaba da gudanar da ayyukansu nagari ga Jami’ar, kasar Nijeriya da kuma al’umma baki daya.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin wata takarar da jami’in hulda da manema labaru na jami’ar Alhaji Jamilu Magaji wanda ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labaru a Brinin Kebbi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *