Jam’iyar PDP Ta Sake Karban Yan Gudun Hijira Kimanin 250 a Gundumar Basawa

Daga Nasiru Adamu

Kamar yadda muka sha kalito muku irin wainar da ake toyawa a tsakanin siyasar gundumar Basawa dake cikin karamar hukumar Sabon gari, jiya lahadi Jam’iyar PDP ta sake karban wasu yan Gudun hijira kimanin mútum 300 da suka cansa sheka zuwa Jam’iyar ta PDP.

Taro ya gudana ne a wurare guda biyu daya an yi shi da safe a unguwar Mangorine inda kimanin mutane 200 suka canza sheka zuwa ciki Jam’iyar PDP karkashin jagorancin Hon Ibrahim Isa Mai Manja.

Ya jawo hankalin matasa da su kasance masu karatun ta natsu a lokutan zabe mai zuwa, domin sanin shuwagabanin da za su zaba wanda za su share masu hawayen da suke fama da shi a halin yanzu.

Sa’annan taron na biyu an gudanar da shi a unguwar Yaldorawa Hayin Dogo Samaru a karkashin jagorancin Hon Jamilu Muhammad Tinau inda mutane kimanin 100 suka canza sheka zuwa wannan Jam’iyar ta PDP

Shima ya baiyyana irin wahalolin da rashin adalci na shuwagabanin Jam’iyar APC ya sanyasu kafewa cikn wannan Jam’iyar ta PDP wadda ta yi mulki cikin kamanta adalci ga kowa da Kowa dake kasar nan

Jim kadan bayan kammala tarukan wakilinmu ya sami zantawa da daya daga cikin shuwagabanin PDP dake wannan yankin Hon Muhammad Awwal Abdullahi Raba yayin da ya yi maná karin haske a bisa nasarorin da Jam’iyar PDP ta samu cikin kasa da watanni 2 inda yace sun karbi bakuncin kimanin mutum 4500 a tsakanin gundumar Basawa Samaru Bomo da Jama’a

Wanda ke nuna mana Juma’ ar da zata yi kyau tun daga laraba take farawa kamar yadda bahaushe ke cewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *