Daga Mansur Aliyu

Jam’iyyar AAC ta bayyana shirinta na tabbatar da cikakkiyar zaman lafiya a kudancin jihar Kaduna da dukkan sassan jihar in har jami’iyyar ta samu nasarar darewa karagar shugabancin Nijeriya a zaben da za a gudanar a watan Fabrairu na shekarar 2023.

Mataimakin dan takarar shugabajnci na jam’iyyar, barista haruna Magashi ya bayyana haka a sakosa na na taya al’ummar Kirristan Nijeriya murnar bikkkin Kirsitimet a kaduna. Ya kara da cewa, yakamta al’umma Jihar Kaduna su hada hanu da jam’iyyyar don kawo karshen matsalar da ake fuskanta a sassan Nijeriya gaba daya.

Ya ce, dan takara shugabanci kasa na jam’iyyar, Omoyele Sowore mutum ne kwararre daya ke da shirin don dawo da zaman lafiya a Nijeriya musammana a yankin kudancin Kaduna da matsalar tsaro tafi addaba.

Kudan kaduna dai yana fuskantar mastsalar tsaro a cikin shekarun nan abijn da ya tarwatsa al’umma yankin tare da haifar da asarar rayuka da dukiya na miliyoyin nairori, ko a makon jiya sai da aka yi jana’izar mutum 40 da ‘yan ta’adda suka kashe a garin Mallagum da Sogwon da ke karamar hukumar Kaura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *