Daga Ibrahim Muhammad Kano

An musanta ikirarinda wani Dokta Muktar Saleh ya yi na cewa shine dan takarar Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar APM da kuma janye takararsa  ga  wani Dan takarar Gwamna a karkashin wata jam’iyyar da cewa ba gaskiya ban

Jam’iyyar APM a jahar Kano ta tabbatarda cewa Janar Ibrahim Sani Yakasai mai ritaya shine halastaccen tabbataccen dan takarar Gwamna na jam’iyyar yana nan kuma akan takararsa.

Sannan kuma jam’iyyar ta APM ta qgargadi Muktar Saleh ya dawo ya janye wadannan kalaman nasa marasa tushe bare makama domin kuwa Janar Ibrahim Sani yakasai mai ritaya ne dan takarar Gwamna na AP

Dan haka yan jam’iyyar sunyi kira ga al’ummar jihar Kano suyi watsi da sanarwar ta gangan su kuma  fito ranar zaben Gwamna, su zabi dan takarar Gwamna na jam’iyyar APM saboda kyawawan manufofinsa  masu nagarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *