Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kamfanin NBC masu yin lemo sun tallafawa Mata a jihar Kano da kayan sana’oi na hannu dan dogaro daka

Matan da suka sami tallafin an zabo sune daga cikin mata da kamfanin ya dauki nauyin basu horo na tsawon mako daya a  fannoni daban-daban na sana’o

A jawabinsa janar Manaja na kamfanin reshen Challawa.Mr.Olisa Oraka yace tallafin na daga tsare-tsaren bukin cika Shekaru 70 da kafa kamfanin a kasarnan da sukayi amfani da damar wajen yin abubuwa na tallafawa cigaban al’umma

Shima Alhaji Muhammad Aminu manaja mai kulada harkokin jama’a na Abuja da jihohin Arewa yace kamfanin na Koka-kola ya yi Shekarau 60 a Kano da kafuwa, kuma dama,suna zabar abubuwa da suke dan tallawa mutane domin cigaban Kan

Ya ce amma,wannan karon horo suka bayar dan bukin cikar NBC  shekaru 70  a kasarnan.Shine suka zabi wasu fannoni da zasu tallafawa cigaban matasa da mata da sauran al’umma a fannin samarda ruwa da kiwon lafiya.da ilimi

Muhammad Aminu yace taron na  bukine domin rufe horo   na tsawon  mako guda da suka  baiwa mata samada 200  akan koyon  yin cincin,kayan kwalliya,sarqoqi da yin takalma da mai na shafawa da sabula

Muhammad yace daga cikin Matanda aka baiwa horonne, aka zavi   25 da sukafi hazaqa a lokacin horon, aka basu  tallafin  kayan  sana’oi dan dogaro daka

Taron ya sami halartar Turakin Kano.Hakimin Dala Alhaji Abdullahi Lamido Sunusi da Hakimin Madobi.Dukkansu sunyi kira ga wadanda suka amfana akan suyi kyakkyawan amfani da tallafin wajen  cigabansu da yan’uwansu harma su rika tallafawa mazajensu

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *