Daga Shu’aibu Ibrahim

Hukumar tsara birane na Jihar Kaduna, (KASUPDA) karkashin jagorancin Alh Sama’ila Dikko ta yaba wa shugaban karamar hukumar sabon Gari , Injiniya Muhammad Usman.

Yabon ya biyo bayan ziyarar bazata da shugaban hukumar tsara birane ta Jihar Kaduna, Alhaji Sama’ila Dikko ya kai sabuwar tashar motar Sabon Gari da ke ‘yankarfe a ranar Asabar.

Sama’ila ya nuna gamsuwarsa ganin yadda aikin  sabuwar tashar yake tafiya babu kama hannu  yaro, musamman yadda ake aiki babu dare ba rana don ganin an samu an kammalawa.

Shugaban ya kuma bada shawarwari musamman kan yadda yake ganin tashar ya kamata ta kasance, tare da jawo hankalin jama’a kan yadda za su amfana da aikin idan an kammala anan gaba.

Ya kuma bukaci injiya Usman da ya kara daura dammara da kauda kai ga surutai ko zagi da za a dinga yi, ya ce saboda duk harkar gyara ta gaji haka.

Da yake tufa albarkacin bakinsa ga wakilinmu, injiniya Muhammad Usman ya nuna farin cikinsa da wannan ziyarar, duk da cewa ba wannan wurin kadai shugaban hukumar ya ziyarta ba ,ya ce sun fito ne don zagaya ayyukan da gwamnatin Jihar Kaduna keyi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *