Daga Umar Faruk Brinin Kebbi

Wata babbar kotun jihar Kebbi da ke zaune a Birnin Kebbi, ta amince da dukkan bukatu da wasu ’yan jam’iyyar PDP 43 da ke cikin korafi suka gabatar a gaban kotun.

Alkalin kotun, Mai shari’a Sabi’u Shuaibu Bala, a cikin hukuncin da ya yanke, ya ce an same shi da bukatar da ta dace kuma kamar yadda aka umarta kamar yadda masu shigar da karar suka nemi kotun da ta amince da wata bukatu guda biyar bisa ga hujojin su.

Masu shigar da kara, Alhaji Abdul-Malik Haliru (Milton) da wasu mutane 42 sun shigar da kara a gaban kotu a kan jam’iyyar PDP da wasu mutane hudu suna addu’ar neman a yi watsi da taron da aka ce an yi daban-daban na zaben shuwaganni na mazabu,  kananan hukumomi da kwamitocin zartarwa na Jihar.

Masu neman takarar sun kuma nemi a ba da umarnin ga jam’iyyar ta PDP na tsaya wa cik har zuwa lokacin da aka kammala sauraren karar da kuma umarnin hana duk wani mamba na wadanda aka kara na biyu bayyana kansa a matsayin mamba na kwamitin zartarwa na kowace shiyya, ko karamar hukuma da Kuma  Jihar biyo bayan zarge-zargen da aka yi na zaben shuwagannin Jam’iyyar tun daga matakin mazaba har ga shuwagabannin na jaha.

Bugu da kari, mambobin da suka fusata sun nemi a ba da umarnin korar wadanda ake karan na nuna rashin amincewarsu na farko da suka yi na cin zarafi ga tsarin kotun.

A hukuncin da aka yanke a kotun bayan sauraron karar korafi da lauyoyin masu kara   da wadanda ake kara suka gabatar, Alkalin kotun, Mai shari’a Sabi’u Shuaibu, ya ce idan aka yi la’akari da gaba daya masu kara sun gamsar da kotu kan abubuwa biyu da ake bukata a cikin bukatar,  na kan bukatun da suka shigar  don haka bukatun sun cancanta  kuma sun gamsar ta kotu  bisa ga  hakan kotu ta amince ga dukkan bukatun da suka nema a a cikin korafin nasu ga dukkan shuwagabannin jam’iyyar PDP tun daga matakin mazaba har zuwa na kananan hukumomin da kuma na jaha da su daina gabatar da kansu a matsayin shuwagabannin har sai an kammala sauraren karar da kuma ba da hukunci, inji kotu.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *