Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sabon Babban sakatare na hukumar kulada tarihi da al’adu ta jihar Kano.Arch (Mazayyani )Ahmad Abba Yusuf y bayyana nauyi da Allah ya dora masa na kulada hukumar abin farin cikj ne da jimami kuma ta wata fuskar, domin mukami na Duniya nauyi da Allah ke dorawa dan’adam da kowa za’a tambaye shi akan nauyi da aka dora masa.

Ya bayyana hakanne da yake zantawa da yan jarida ciki da jaridar Idon mikiya/factual.Ya kuma godewa Allah bisa irin kyakkyawan niyya da yasa masa yake tare da hada shi da mutane nagari da suke tare da zasu rika bashi shawarwari kuma Allah baya dorawa mutum abinda ba zai iya ba yana kuma gode masa da ya bashi mukamin ba dan yafi kowa ba,ba kuma dan komai ba, sai dan wasu al’amura da ubangiji shi ya barwa kansa sani.

Ya ce al’ada da tarihi na daga kashin bayan cigaban kowace al’umma, duk al’umma da ta rasa tarihinta da al’adarta, babu inda za ta je a cikin zarafin cigaba.A rayuwa na Duniya tarihi,al’ada da yanayin zamantakewa wasu ginshikan abubuuwa ne da kasashe da suka cigaba ake kallonsu a wayayyayu shi suka rike suka kawo inda suke ake kallonsu da sha’awarsu.

Ya.yi nuni d a cewa da munada wurare a wannan jihar na tarihi da al’adu da wurare da kayayyaki na tarihi, in aka rike aka inganta su za’ayi mamakin yanda zamu zama a cigaban rayuwa.

Arch Ahmad Abba ya ce abin takaici ne yanda hukumar tarihi ta zama a wajen wasu ma’aikata duk wanda aka kawo wajen tamkar an bashi horo be, saboda wajen ba hada-hada ta samun kudi,saboda wasu ma’aikata na duba me za’a samu ne ko ta wane hali wannan na daga illar rashin sanin kai da make dashi.
Ya yi nuni da cewa da an san muhimmancin wajen da ma’aikata nema zasu rika yi a kawo hukumar.Amma. xuwansa da yardar Allah zai yi kokarin yin. abinda yakamata na bunkasa hukumar ta yi gogayya da sauran kasashen Duniya.
Yanzu haka ma za su sa kayan sadarwa na zamani da zasu taimaka.wajen jawo hankalin mutane daga sassan Duniya ta susan al’adu da tarihin Kano da zai jawo hankalinsu su rika zuwa yawon bude ido.

Ya ce za su kawo gyara tun daga matakin gyara ma’aikatar da aka bar muhallinta ba gyara tsawon lokaci ta yanda zata koma mai yanayi mai kyau ma’aikata za suyi aiki cikin natsuwa da walwala da hakan zai sa a rika sha’awarta.

Mazayyani Ahmad Abba Yusuf ya ce gwamnan jihar Kano mutumne mai sha’awa da son raya al’adu yana dai hangen nesa ya san muuhimmancin tarihi yana yi masa fatan Allah ya bashi dama na aiwatar da kudurori na ciyarda jihar Kano gaba,da su kuma zasu bashi gudummuwa sosai dan cimma burinsa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *