Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kungiyar ‘Yan arewa masu fafutikar ganin ana gudanar da kyakkyawar Shugabanci.
(Arewa Movement for Good Governance. AMGG)da ke kokarin tabbatar da kyakkyawan shugabanci ta hanyar gaskiya da rikon amana ta yi Allah-wadai da wani rahoto da ta ce kirkirarre ne da wata kungiya da ta kira kanta da suna Gamayyar ‘Yan Jarida ta Yammacin Afirka masu binciken kwakkwafi ( coalition of West Africa Investigative Journalist ) sukayi dan bata sunan yan Arewa da ke kan manyan mukamai a hukumomin gwamnati daban-daban a kasarnan.

Wannan na cikin wata takarda da shugaban kungiyar Umar Usman ya sanya hannu aka rabawa manema labarai ciki da jaridar idon mikiya.

Takardar ta yi bayani akan irin rahotanni na kage da nufin muzantawa da bata suna da mutuncin yan Arewa da kungiyar tayi akan yan Arewa dake kan manyan madafu a gwamnatin tarayya.

kungiyar ta AMGG ta ce irin wannan rahoton ya saba da ka’ida ta aikin jarida kuma bai dace ba a cikin kasa da take da wayewa mai bin tsarin mulki na damakwaradiyya irin Najeriya.

Takardar ta bayyana cewa kungiyar da ta kira kanta wai gamayyar yan jarida masu bin kwakkwafi na Afirka ta Yamma sun kirkiri irin wannan rahoton ne kawai mara tushe da rashin kan gado kawai da wani mummunan nufi domin a bata sunan ’yan Arewa da ke kan manyan mukamai a kasarnan.

Kungiyar ta AMGG ta ce tun bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinibu ya zama shugaban kasa,irin tsare-tsare da ya bijiro dasu masu tasiri sun gamsar da mafi yawan ‘yan Nijeriya ciki har da ‘yan adawa da fatan cewa tabbas kasar nan ta dauki hanyar cimma nasara duba da matakai na sauye-sauye da yawa da yazo dasu masu amfani ne.

Ta zargi kungiyar gamayyar da ta kira kanta na yan jarida ta Afirka ta Yamma masu binciken kwakkwafi da cewa ta saba ka’idar aikin jarida ta yin shifting gizo ba ta yi bincike na adalci ba kan zargin da suke yi wa hukumomi da dama a Najeriya musamman wanda ‘yan Arewa ne ke shugabancinsu.

AMGG ta zargi kungiyar da suka fake da sunan masu bin kwakkwafi yin bincike da cewa wasu ne ke daukar nauyin su dan kitsa shirin kawo rarrabuwar kawuna da tayar da fitina a kasar nan da ke da dinbin al’umma ta kirkirar rahoto da bayanai na karya akan ‘yan arewa da ke rike da manyan madafu a kasarnan saboda son zuciya.

Kungiyar ta yan Arewa masu rajin tabbatar da mulki na adalci sun ce wannan dai ba shi ne karon farko da irin wadànnan kungiyoyi da ake daukar nauyinsu su kai hari ta kirkirar bayanai na karya da nufin bata masu rike da manyan madafu a kasar nan yan Arewa.

Kungiyar ta AMGG ta yi kira ga yan Nijeriya akan suyi watsi da Allah-wadai da irin wannan zargi na karya mara tushe da ake daukar nauyin wasu su kirkira dan batanci ga masu rike da manyan madafu yan Arewa domin cigaba da samun hadin-kan kasa da zaman lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *