Daga Bello Hamza

Kungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Oyo ta bukaci shugabanin coci-coci a fadin jihar su umarci al’ummarsu da su fara azumi da addu’o’i na kwanaki 7 don neman zaman lafiya ga kasar mu Nijeriya.

A ranar Juma’a ne shugaban kungiyar reshen jihar Oyo, Apostle Joshua Akinyemiju ya yi kiran ya kuma ce, za a fara azumin ne daga ranar 18 ga watan Yuli.

Ya kuma bayyana cewa, a rana ta 8 za a gudanar da tarukan godiya a bisa yadda Allah ya amsa addu’o’inmu.

“Babban burinmu na addu’o’i’n shi ne na Allah Ya zaunar da kasar nan lafiya da kuma Jihar mu ta Oyo.

“Wananan addu’ar na da muhimmanci, Allah ya tsirar da mu ya kuma karya dukkan makiyan Nijeriya,” in ji shi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *