Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kungiyar dalibai karkashin jagorancin Amirah Sarah Bashir Galadanci sun gudanarda taron bita na kwana biyu domin zaburarda dalibai akan muhimmancin karatun Qur’an.

Taron wanda ya gudana a jihar Kano ya sami halartar  dalibai daga sassa da dama daga jihohin kasar nan

Da take bayani gameda makasudin taron Amirah Sarah Bashir Galadanci tace dan  gyara dangantakarsu da Qur’ani da yin azama wajen haddace shine da aiki dashi yasa sukayi taro

Ta ce yanda haduwa take hada makarantar Kur’ani, musamman in ana musaffa sai kaji karin natsuwa da dadi da kauna a tsakaninsu, hakan yasa ta ji shaukin su hada wannan taro da suka gudanar na kwana Biy

Amirah Sarah Bashir Galadanci tace malamai da dama sun gabatarda mukaloli daban- daban da suka shafi tasiri da abin al’ajabin Kur’ani da kuma muhimmancin baiwa Kur’ani lokaci da yanda za’a dauki matakai na yin hadda da sauran fannon

Ta ce taron ya sami halartar dalibai daga jihohin kasarnan na jami’oi da sakandire maza da mata da  suke fatan ayi amfani da abubuwa da aka koya wajen kara musu himma da kwazo da shauki, wajen karatu da aiki da Qur’ani.Kuma nan gaba za su cigaba da shirya taro makamancin wannan.

Amirah Sarah Bashir Galadanci ta godewa dukkan masu ruwa da tsaki da suka bada gudummuwa wajen shiryawa da gudanarda taron da akayi cikin nasara.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *