Daga Shu’aibu ibrahim Gusau

Kungiyar lauyoyin Najeriya NBA reshen jihar Zamfara ta bukaci mambobinta lauyoyi da su kasance masu kwarewa da kwazo da kuma gaskiya akan aikinsu.

Hakan na zuwa ne yayin da kungiyar reshen jihar Zamfara ta karrama lauyoyi shida da suka hada da Babban Lauyan Najeriya (SAN) na farko a jihar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Gusau, jim kadan bayan rufe Taron bikin na makon Lauyoyi na Wannan shekarar 2022 a jihar, shugaban kungiyar ta NBA, Barista Junaidu Abubakar ya bayyana cewa an dauki tsawon mako guda ne domin tsaftace sana’ar tare da bayyana ayyukansu ga jama’ar jihar.

Ya bayyana cewa, reshen ya gudanar da jerin laccoci tare da taron karawa juna sani da Kuma wasan kwallon kafa na sada zumunci da liyafar cin abinci ga mambobin da abokai da masu fatan alheri a fadin jihar.

A cewarsa, reshen ya yi amfani da bikin wajen karrama wasu fitattun kwararrun lauyoyi guda shida wadanda suka sadaukar da kansu ga bil’adama a jihar da kasa baki daya.

Ya yi kira ga jama’a da su rika ganin lauyoyi a matsayin abokai wadanda a kullum suke fafutukar tabbatar da adalci ga kowa ba tare da la’akari da addini da kabila ko yanki ba.

A cewar sa “Aikinmu shine tabbatar da adalci ga kowa da kowa, ina kira ga jama’a da su kalli sana’ar mu a matsayin hidima ga bil’adama”.

Wadanda aka karrama sun hada da SAN na farko a jihar, Abdulaziz Sani Mohammed SAN, sakataren hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta (ICPC), Farfesa Musa Usman Abubakar saboda nasarorin da suka samu.

Sauran sun hada da babban alkalin jihar, Mai shari’a Kulu Aliyu OFR, mai shari’a Lawal Garba na kotun koli, Shaawanatu Mohammed Ahmad Esq a matsayin babbar lauya mace, kamaluddeen Mohammed Esq a matsayin matashin lauya mai aiki da AA Jibril Esq a matsayin babban lauya a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *