Daga Nasiru Adamu

Ranar Asabar din da ta gabata né gungiyar Mata zalla da ta hada da palladan da Unguwar fulani zariya ta yi wani gangamin bikin kona tsintsiya tare da karban wasu Sabbin yayan kungiyar da sukayo gudun hijira daga Jam’iyar APC.

Shugabar Matan gungiyar Malama  Rukayya Inusa ta yi wa wakilin mu karin haske akan manufar wannan gangamin da matan suka gudanar kamar haka.

Mun kasance a zaben da aka gudanar a shekarar 2015 mun yi ruwa  da tsaki domin ganin Jam’iyar APC ta ci zabe sakamakon amincewar da muka yi mata ashe yaudarar mu akayi, mun yi tsammanin yadda tsintsiya ke yi mana ammfani a gidajen mu wajen tsabtace muhallan mu haka zata ci gaba da yi mana har cikin birni da Kauyukan mu inji ta.

Malama Rukayya ta ci gaba da cewa sakamakon bakin mulkin da wannan Jam’iyar mai tambarin tsintsiya ke gudanar, Mata da haka sun rasa mazajen su sakamakon rabuwan aure, haka nan mazaje da yawa sun gudu sunbar iyalinsu sabo da rashin abinci, milyoyin kananan yara sun rasa iyayen su, an kori mutane daga ayyukan su kuma ba’a samarwa da kowa komaiba. Sakamakon haka yau mu kungiyar mata zalla dake Pallada da Unguwar Fulani muka yanke shawarar canza sheka zuwa Jam’iyar PDP mai adalci, domin ta ti abaya mungani.

Kuma ayau karkashin wannan kungiyar mun karbi matan kimanin 4712.dun haka kamar yadda muka yiwa APC ruwan kúri’u a shekarar 2015 muka Kaita sama, haka zamu janye mata ruwan kuri’u mu Kaita kasa insha Allahu

Hakanan anashi jawabin Sa Sakataren Stekholda na gundumar Basawa Hon Sulaiman Safiyanu ya yi kira ga sauran matan da basu shigo wannan jám’iyar  PDP Na,am,  da suyi gaggawar dawowa cikinta domin taimakawa wajen kawar da zalunci da ake yi a wannan kasar .

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *