Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sakamakon wata badakala da shugabanin Kwamitin Dattawan jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Fagge a jihar Kano, (Caucus) sun dakatar da shugabansu, Alhaji Ali Baba Agama Lafiya Fagge bisa zarginsa da danne musu haƙƙoƙinsu da yayi har karo biyu.

A Cikin wata takarda mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na kwamitin da mataimakinsa, Salisu Shitu da Shehu Sani Chidozie, da aka aikewa shugaban karamar hukumar Fagge, Ibrahim Muhammad Shehi, sun bayyana cewa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya basu Naira Miliyan daya (N1,000,000) da Sallar da ta gabata ta hannun dakataccen shugaban nasu, amma shiru bai basu ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, kwanan nan ma jam’iyya ta basu Motoci guda Ashirin domin halartar taron zuwan dan takarar shugabancin Nigeria na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, na ziyarar kwanaki biyu da yayi a Kano, shima dai shiru bai basu haƙƙin su ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *