Daga Ibrahim Muhammad Kano

Jigo kuma daya daga cikin yan gaba-gaba wajen bada gudummuwa a tafiyar siyasar kwankwasiyya a jihar Kano.Hon.Munzali Abubakar Danbazau ya bayyana cewa irin kyawawan manufofi da kuma son cigaban al’umma na Injiniya Dokta Rabiu Kwankwaso yasa suke bin sa sau da kafa.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da yan jarida a Kano ya kara da cewa abinda ya basu kwarin gwiwa, shine irin tafiya da akayi a 2011 zuwa 2015 da Kwankwaso ya yi Gwamna ya kawo cigaba ga Matasa da Mata da abubuwa na alkhairi da yawa akayi ya basu kwarin gwiwa wajen tallata yan takara na NNPP tun daga kan takarar shugabancin kasa da Kwankwaso ya yi har yan majalisun Dattawa dana tarayya da jiha da na Gwamna.Abba Kabir Yusuf.

Ya yi nuni da cewa harkar kulada lafiya da ilimi da koyawa Mata da matasa sana’oi da basu jari da jawo masu sana’oi daban-daban, kama daga mahauta da wanzamai da masu walda da sauran sassa na yan kasuwa da dama da aka taba aka kyautata musu ta suke tafiyar.

Munzali Danbazau yace sai da abin takaici, bayan tafiyar Gwamnatin Kwankwaso a karkashin mulkin Ganduje ba’a cigaba da irin wadannan ayyuka ba,shi yasa ma mutane suka gaza gansuwa da Gwamnatin,aka ki zabarta a yanzu saboda muzgunawa al’umma da saba alkawari da akayi na kin dorawa a tsarinda Kwankwaso ya taho da shi tun 1999 aka dora a 2011.

Ya ce wannan irin kishi na Kwankwaso ne ya basu kwarin gwiwa suka ce bari su taimaka da abinda suke dashi da lokacinsu wajen tallata yan takararsu na NNPP.Tun daga kan Kwankwaso har injiniya Abba Kabir Yusuf har aka kai ga wannan nasara.

Hon.Munzali Abubakar Danbazau ya ce zabe da aka yi wa Abba Kabir Yusuf a zaben 2019 kuma aka hana al’ummar Kano zabinsu ya kara musu kwarin gwiwa ne ma na dada jajircewa a tafiyar kwankwasiyya.

Ya ce sannan ya dadawa dan takararsu na Gwamna sake samun kwarewa da gogayya a harkar siyasa, ya sake samun wata dama ta sanin abubuwa da a baya bai sani ba, da sake cudanya da yan’siyasa manya da matsakaita da kanana.Sannan ya kara gogewa akan harkar gudanarwa na mulki.

Yace Abba sun jima da Kwankwaso tun 1999 zuwa yanzu a baya ma anso a tsayar dashi takarar Gwamna tun a 2015 amma wasu mutane suka karkata kan Ganduje za’a tsayar, shi kuma jagora ya ce a tafi a hakan aka tsaida Ganduje a wancan lokacin.

Ya yi nuni da cewa duba da yanda mutane suka fito suka baiwa Abba goyon baya, suna da kyakkyawan zato da tunanin ce wa za’a sami sauki da rangwame a cikin tafiyar kwankwasiyya fiye da ta wannan Gwamnati mai barin gado da ake da ake, wanda dama tun asali tare suke, suka balle.Amma hakan ba zai sa in sun dawo sun gane gaskiya a sake rungumar su ba, a hadu a hada karfi da karfe a ciyarda Kano gaba wannan shine burin Dokta Rabiu musa Kwankwaso na ganin dan talaka ya sami cigaba ya taimaki kansa da al’umma.

Hon.Munzali Abubakar Danbazau ya kara da bayyana cewa ya’yan talaka a lokacin mulkin Dokta Rabiu Musa Kwankwaso da yawa sun sami dama na zama likitoci,da matuka jiragen sama da sauran fannoni na kwarewa da ko a mafarki basu taba tunanin haka ba.Wannan ya sa Kwankwaso yake samun karfin gwiwa da bugar kirji ko’ina yaje yake tawassali da irin ayyuka da ya yi saboda irin hangen nesa da yake da ita,wanda da ba abin alkhairi ya kyankyashe ba, da yanzu abinda ya yi shi zai rika binsa.

Danbazau ya ce, irin wannan abin alkhairi da Kwankwaso ya shuka, shine yake girba, a wannan zabe na 2023 an sami nasarori akan Sanatoci guda biyu na Kano ta tsakiya da Kano ta yamma da yan majalisun tarayya da ba jiha da Gwamna.Zabe ma da za’a karasa nan gaba in Allah ya yarda zasu sami nasara gaba daya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *