Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool Ta doke takwaran ta Manchester City a gasar cin kofin Community Sheild. Wasan ya gudana ne a filin wasa na King Power Stadium dake Ingila da mu yammacin yau Asabar.

Liverpool ce ta fara zura ƙwallo ta hannun dan wasa Arnold, daga baya sai Julian Alvarez dan Manchester City ya farke. Bayan wasu mintuna ne Liverpool Ta samu Penalty inda dan wasa Muhammad Sallah ya zura ƙwallon ba tare da gargada ba. A karshe kuma Sabon dan kwallon da Liverpool Ta siya ne ya zura ƙwallon karshe inda aka tashi 3-1.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *