Daga Nasiru Adamu

Rananar lahadin karshen makon da ya gabata ne shahararriyar Makarantar nan mai suna Ummu Tahfizul Kur’an dake layin Mai Unguwa Kakale Hayin dogo Samaru Zariya ta yi bikin yayen dalibai 12 a karo na farko.

Taron wanda aka gudanar da shi a harabar makarantar ya sami nasaran halastan manyan Malamai da Sarakunan tare da yan siyasar cikin garin Samaru da kewaye.

Malam Isma’ila Zakri Alkishnawi daga Katsina, shi ya kasance babban bako mai jawabi, yayin da ya yi tsokaci akan muhimmancin karatun alkur’ani da yin aiki da shi, kuma ya janyo hankalin daliban su ci gaba da nazartan alkur’ani, domin su kasance Malamai nan gaba

Hakanan daya daga cikin shuwagabannin wannn makarntar Malam Yusif Nadabo, ya jawo hankalin iyayen daliban, don su kasance masu sauke hakin Makaranta, domin yin hakan yana  daga cikin samun albarkan karatun dalibi

Haka nan ya nuna takaicinsa dangane da iyaye ke muhimmatar da biyan makudan kudade a makarantun Boko wanda babban sakamakonsa bai wuce neman abinci ba.

Amma yan kudaden da ake badawa wanda bai wuce naira dari ko dari biyu a makarantun da mutum zai sami rayuwa ta dundundun sai akasa biya, wanda hakan bai kamata ba injishi.

Shima a nashi jawabin shugaban Makarantar Malam Awwal Kunkumi bayan ya  karanta tarihin kafa Makarantar, daga bisani ya baiyyana nasarorin da Makarantar ta samu wajen samar da nagartatun dalibai sana da 700 masana alkur’ani da fassaransa tun daga wancan lokacin har ya zuwa yau da ake bikin yayen farko a cikin tarihin ta.

Saidai daga bisani ya nuna takaicinsa na kalubalen da makarantar ke fuskanta tsawon wannan zamanin har yanzu bata mallaki ko kafa daya ba na muhallinta, wand ya ce sakacin masu hannu da shuni ne da kuma iyayen dalibai, da shuwagabanin al’umma .

Daga karshe ya yi kira ga masu euwa da tsakin makarantar da su kara jajurcewa wajen ganin wannan makarantar ta sami mohallinta nan bada dadewa ba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *