Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta yi nazari tare da farfado da ayyukan ofishin hulda da jama’a domin samun ingantacciyar alaka da abokan hulda .

Wannan yana daukene cikin wata takarda Mai dauke da sa hannun jami’in hudda da jama’a na majalisar,Alh Nasiru Biyabiki ,wanda ya rabata ga mamema labarai, yace shugaban majalisar Rt. Hon. Nasiru Mu’azu Magarya (Tafidan Kanwa) ya bayyana hakan ne a lokacin da yake duba chamber da ofisoshin Membobi da Ma’aikatan Majalisa.

Ya ce samun irin wannan muhimmin ofishi a Majalisar zai ba da damar yin aiki mai yawa bisa gogewa da goyon baya na waje da na cikin gida ta hanyar inganta dokokin da suka shafi mutane.

Magatakardar majalisar da mataimakinsa Alh. Shehu Sa’idu Anka da Alh. Mahmud Aliyu sun yabawa ma’aikatan bisa jajircewarsu wajen gudanar da ayyukansu ya kuma yi kira garesu da su ci gaba da gudanar da ayyukansu.

A yayin ziyarar tasa, Tafidan Kanwa, ya bada tabbacin shirinsa na inganta jin dadin ma’aikatan domin kara musu kwarin guiwa, za’a kula da ma’aikatan da suka cancanta da kuma hukunta masu yin magudi a cikin ma’aikatan, yace ba za mu lamunci lalaci ba.

Magatakardar Majalisar Alh. Shehu Sa’idu ya godewa shugaban majalisar tare da yaba masa bisa gudanar da wata manufa ta bude kofa, wanda a cewarsa za ta ba da damammaki na shawarwari da nasihohi da za su sauya yanayin aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *