Daga Ibrahim Muhammad Kano

An bayyane Mata sune na kan gaba da zasu amfana a wannan Gwamnati ta Injiniya Abba Kabir Yusuf duba da irin jajircewa da gudummuwa da suka bayar dan tabbatar da nasarar sa.
Hajiya Fatima Abubakar Abdullahi wacce daraktar yakin Neman zabe na wayar dakan mata na takarar shugabancin kasa na Fokta Rabiu Musa Kwankwaso da kuma na zababben Gwamna Injiniya Abba kabir Yusuf na Kano ta tsakiya ta bayyana hakan ga manema labarai a taron ya ye wadanda Hajiya Wasila Aibo ta horas akan sana’oi.

Ta yaba da iron kokarin Hajiya wasila wacce daya ce daga mambobinta wajen koyawa matasa sana’a.

Fatima ta ce a tafiyar su ta kwankwasiyya dama babu masu zaman banza, sunada sana’oi basa jira dama sai wani ya basu wani abu domin jagoransu Dokta Rabiu Musa kwankwaso ya koya musu amfanar da al’umma shi yasa duk sana’ar da sukeyi sunakokarin saukarwa kasa su koyawa matasa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *