Daga Muhammad A. Abubakar 

A ranar Litinin ne sabon gwamnan jihar Zamfara, Dauda Dare, ya koka, yana mai cewa bai samu ko sisi ba a baitul malin gwamnatin jihar.

Dare, wanda ya bayyana haka bayan rantsar da shi a filin baje kolin kasuwanci da ke Gusau, ya jaddada cewa bai samu komai ba a baitul malin jihar ba a lokacin da ya karbi ragamar mulkin jihar daga hannun magabacinsa Bello Matawalle.

“Ina son na sanar da al’ummar jihar cewa, ban tarar da komai ba a baitul malin jihar.

“Na kuma gaji dimbin basussuka da lamuni da suka kai biliyoyin nairori.

“Saboda haka, ina kira ga al’ummar jihar da su kara hakuri tare da ba ni cikakken goyon baya da hadin kai a wannan lokaci mai wahala.

“Na yi alkawarin kawo ci gaba cikin sauri a jihar a lokacin yakin neman zabe musamman ta fuskacin tsaro, ilimi, samar da ayyukan yi, lafiya da kuma noma.

“Na zo ne domin ceton jihar Zamfara da yardar Allah kuma zan yi iya kokarina wajen ciyar da jihar gaba.”

Sabon gwamnan ya kuma yi kira ga matasa da su guji duk wani nau’in miyagun ayyuka.

Matawalle da mataimakinsa Hassan Nasiha ba su halarci bikin rantsarwar ba.

Matawalle dai ya fice daga jihar tun lokacin da ya fadi zaben gwamna.

By Editor

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *