Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamna Bello Muhammad Matawallen, ya Jinjinawa Jama’ar Gummi , Ganin yadda suka fito kwansu da kwarkwatansu domin su amsa kiranshi.

Bello, ya yi wannan jinjina ne a garin Gummi a lokacin da ya tafi gurin Yakin neman zabensa a garin na

Gummi, ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC Gummi bisa yadda suka amsa kiran da akayi masu na Gudanar da gangamin neman jam’iyyar APC ta maimaita Karo na biyu.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su sake zaben shi a karo na biyu, domin samun daman cigaba da ayyuka da manufofin sa.

Matawalle ya kara da cewa, “Ina kira gare ku da ku zabi dukkan ‘yan takarar APC a kowane mataki.” yace ya kuma yi alkawarin yin bakin kokarinsa wajen inganta harkokin tsaro da ilimi da fannin lafiya da kuma tattalin arzikin jihar baki daya.

Tun da farko shugaban kungiyar yakin neman zaben Matawalle karo na biyu, Abdul’aziz Yari ya yabawa al’ummar karamar hukumar Gummi bisa kauna da goyon bayan da suke baiwa jam’iyyar APC.

Yari ya ce, APC zata ci gaba da zama jam’iyyar siyasa mai karfi a jihar domin ‘yan adawa ba su taba cin zabe a jihar ba.

Yari ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da su ci gaba da ba da hadin kai tare da tabbatar da yin aiki don samun nasarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *