Daga Ibrahim Muhammad Kano

Sakamakon zaben karashe da aka gudanar na kujerar majalisar tarayya ta Karamar hukumar Fagge ta tabbatarda Batista Muhammad Bello Shehu Fagge be ya lashe zaben.

Da yake bayyana sakamakon zaben, Baturen zaben Ibrahim Tajo Suraj, ya ce MB Shehu ya samu ƙuri’u 19,024 daga jimillar ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da ɗan takarar Jam’iyyar Labour, Shuaibu Abubakar ya rufa masa baya da ƙuri’u 12,789.

Sakamakon zaɓen ya nuna Aminu Sulaiman Goro na APC, shi ne ya zo na uku da ƙiri’u 8,669.Bayan cika duka sharuɗɗan da doka ta tanadar da kuma samun ƙuri’u mafi rinjaye, Barrister MB. Shehu na NNPP ne ya lashe zaɓe,” in ji Baturen Zaɓen.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *