Daga Bello Hamza

Cibiyar lafiya ta MGK Healthcare ta gudanar da taron wayar da kan al’umma tare da yi musu gwajin cutar hanta kyauta.

Taron ya gudana ne a ranar Asabar 30 ga watan Yulin 2022 a harabar asibitin a Kano.

Babban Jami’in gudanarwa na MGK Healthcare, Pharm. Isma’il Usman wanda ya wakilci Babban shugaban Asibitin, Muhammad Garba, ya shaidawa manema labarai cewa sun shirya wannan taron ne domin wayar da kan al’umma kan cutar ta hanta tare da karfafa su akan muhimmancin yin gwajin cutar domin samun kariya daga kamuwa da cutar tare da sanin maganin cutar tare da kuma yi musu gwajin cutar a kyauta.  Inda ya ce; “domin mu tuna ranar Hanta ta duniya. Ranar hanta ta duniya ana tunawa da shi ne a ranar 28 ga watan Yulin kowacce shekara. Sannan a kowacce shekara akwai take da hukumar lafiya ta duniya take fitarwa na abin da za a maida hankali a kan shi. A wannan shekarar hukumar lafiya ta duniya ta fitar da sabon take na ‘kusanto da karfafa gwaji da kuma samar da magani ga mutane’”, ya lurantar.

Ya ci gaba da cewa; “Mun kalli wannan wani abu ne da za mu bayar da gudummawa wajen samar da lafiyayyar al’umma domin ganin cewar an kiyaye mutane daga kamuwa daga wannan cutar. Wanda suke da ita kuma a yi kokarin gano ta a kuma samar musu da hanyar da za su iya samun magani da shawarwari”.

Ya kara da cewa; “Wannan shi ne makasudin da ya sa muka gayyaci al’umma domin su zo mu ba su wannan horaswa da tantance su a kyauta. Sannan mu ba su sharwawari ga wadanda ba su da ita domin su samu hanyar kariya daga kamuwa daga wannan cuta”, ya tabbatar.

Ya jaddada adadin mutanen da suka yi wa wannan gwaji a kyauta, inda ya ce; “akalla mun yi ma mutum 131 wannan gwaji a yau a kyauta”.

Da ya juyo dangane da shawarwarin da suke bai wa al’umma kan wannan cutar kuwa, Pharm Isma’il ya ce; “cutar hanta cuta ce wacce mutane da dama suna dauke da ita ba tare da sun sani ba. Wasu da dama suna yawo da ita ba su san ma suna dauke da ita ba. Kididdiga ta nuna cewar akalla duk dakika 30 ana samun mutum daya da yake mutuwa a dalilin cutar da ke da alaka da cutar hanta”, ya nusasshe.

Ya ci gaba da cewa;  “shawararmu ga al’umma shi ne su farga su kuma yi kokarin zuwa asibitoci domin a tantance su a tabbatar musu ko suna da wannan cuta ko ba su da shi.

Ya yi takaitaccen bayani dangane da rabe-raben cutar hanta da yadda ake kamuwa da ita. Tare da zayyano irin aikin da hanta take yi a jikin dan Adam. “Hanta ita ke sarrafa abincin da muke ci da sha na yau da kullum, ta maida su yadda za su yi aiki sannan ta gabatar da su ga jiki. Wadansu abubuwan da za su iya illata jikin mutum ita ke canza su ta maida su yadda ba zai illata jikin ba,” ya lurantar.

Ya nuna illar dake cikin a ce hantar mutum ta kamu da ciwo, inda ya ce; “daga lokacin da hanta ta illatu, zai zama dukkanin bangarorin jikin mutum zai zamo cikin illa.

Ya shawarci mutane da su rika zuwa asibiti akan lokaci domin a gwada su a tantance su domin gujewa kamuwa da cutar ko illata jikin mutum daga cutar. Sannan ya ce a sani cuta ce da ake iya daukarta daga jikin wani.

A karshe ya yi bayani dangane da ayyukan asibitin na MGK Healthcare, inda ya ce asibiti ne na kwararru da yake yin ayyuka daban-daban. Kuma suna da kananu da manyan likitoci da suke duba marasa lafiya daban-daban wadanda suka hada da masu zuwa a duba su su koma gida, da ma wadanda ake kwantar da su har sai sun samu lafiya.

Sannan ya ce daga cikin ayyukansu suna da bangaren masu kula da ciwon hakori, bangaren bayar da magunguna, bangaren gwaje-gwajen cututtuka manya da kanana, bangaren da ke haska cututtukan dake jikin mutum, sannan suna yin tiyatar da ya hada da na kashi, karbar haihuwa, na cututtuka, na kwakwalwa da jijiya da kuma na zuciya da sauran su.

“Sannan muna dauko marasa lafiyar da suke da bukatar taimakon gaggawa zuwa asibiti da motar daukar marasa lafiya wanda ake tafiya da ma’aikatan asibitin a cikinta. Sannan muna da gidauniyyar da take bai wa al’umma marasa karfi gudummawa a bangaren ilimi, kiwon lafiya da kuma muhalli”.

Har wala yau ya ce suna da lasisi a bangaren inshorar lafiya da gwamnatin Tarayya da ta jihar Kano da ma kamfanoni, wadanda ma’aikatan dake karkashin wadannan ke zuwa asibitin ana kula da lafiyarsu musamman wadanda suke karkashin inshorar lafiya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *