Ta Umarci Hadin Kai A Tsakanin Hukumomi

Zamu Tabbatar Da Cigaban Nasarorin Da Aka Cimma – Jamoh

Daga Bello Hamza

Ministar Sufuri Sanata Gbemisola ta kai ziyara na musamman Hukumar Kula da Teku da Tabbatar da Tsaron Ruwan Nijeriya (NIMASA), inda ta zagaya don ganin yadda al’amurra ke tafiya a sahen, wuraren da ta ziyarta sun hada da sashen gudanarwa da harkokin hukumar (NIMASA Command), sashin tafiyar da ayyuka da bangaren kwanfuta (Control and Computer Centre (C4i)) da wurin ajiye jiragen ruwa (NIMASA Modular Floating Dockyard), da kuma dakin karatu na zamani (NIMASA E-library and Vessels) da wuraren da ake gudanar da ayyukan cigaba da ma’aikatar vangarenta da ke rundunar sojin ruwa na yankin Victoria Island.

Ministar ta nuna jin dadinta a kan kayan aiki da na’u’rorin da ta gani a NIMASA, ta kara da cewa, wannan na kara nina irin yadda gwamnatin tarayya na dora muhimmanci ga harkar samar da tsaro da yaki da ‘yan ta’adda a sararin ruwan kasar nan.

Ta kuma yaba wa hadin kan da ke tsakanin hukumomoin gwamnati a bangafren harkokin teku, ta kuma nuna jin dadi a kan yadda ba a samu wata matsala na barayin teku ba a wannan shekarar.

Daga nan ta ce, “Fiye da shekara 28 ake ta yada kasar nan a kafafen yada labarai a kan batun sace-sacen teku a zirinn tekun Guinea (Gulf of Guinea (GoG)”. A shekarar da ta wuce ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Shirin ‘’DEEP BLUE PROJECT” a cikin dan karamin lokaci kuma an samu karya kwatrin don a cikin wata 5 da suka wuce ba a samu wani hari ba na barayin teku, wannan yana tabbatar da nasasrar da NIMASA ta samu a ayyukanta”.

Sanata Saraki ta nuna bukatar a kara zage damtse don jawo hankulan masu zuba jari, musamman ganin yadda take kokarin samar da yanayin da za a gudanar da harkokin a cikin sauki.

A nasa jawabin shugaban NIMASA Dakta Bashir Jamoh ya bayana cewa, babban burin hukumar shi ne tabbatar da cigaban nasarorin da aka samu a baya, sun kuma yi shirin samar da ayyukan da za su gudanar da su na dogon zango.

A halin yanzu zamu fuskanci tabbatar da nasarorin da muka samu a baya “Muna da tabbacin cewa shirin nan na inshorar kayyakin da ake shigho da shi kasarnan zai samu nasara, kasashen duniya sun zura ido suga yadda zamu cigaba da yaki da barayin teku.

Mun kafa hadakar kungiyar masu ruwa da tsaki da suka hada da INTERTANKO, kungiyar masu tanka mafi girma a duniya, da INTERCARGO, kungiyar masu shigo da kayyaki mafi girma a duniya kuma cikin manyan masu dakon man fetur a duniya, muma tattaunawa da su akai-akai a kan cigaban da muke samu a bangaren harkokin teku. Mun kuma karfafa dangantakarmu da rundunar sojin ruwa. Hukumar ‘SHADE Gulf’ wata hadaka ce na tabbatar da tsaro a yankin Guinea inda kungiyoyi kamar su ICC da Kungigiyar Turai ke hada hannun don tabbatar da tsaro a yankin.

Duk da cewa, an cire Nijeriya da cikin kasashen da suka fi hadari a a duniya ranar 3 ga watan Maris, kasashen duniya za su so suga an tabbata a kan aikin da aka yi a baya. Fatan mu shi ne zuwa watan Satumba ya zamana an magance batun ‘War Risk Insurance’ da kuma dukkan matsalolin da suke kawo cikas a harkokinmu” in ji shi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *