Daga Ibrahim Muhammad Kano

Zababben dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Tarauni.Hon.Muktar Umar Yarima ya bayyana cewa abinda ya ja hankalinsa yake bada tallafin duba marasa lafiya da basu magunguna shine lura da yawanci mutane suna fama da larurai da ba za su iya samun magani ba.

Yace ya lura Idan ya je gaishe-gaishe sai ya samu yawanci mutane da  ya je wajensu basuda lafiya ko kuma a gidansu akwai marasa lafiya.Ya ga akwai damar da zai iya taimakawa mutane ba sai  lallai yana kan wata kujera ba zai iya taimakawa mutane, shine yasa suka dauki wannan layin suka fara  taimakawa mutane a harkar lafiya

Hon. Umar  Muktar Yarima ya ce Allah ya gani har a  zuciyarsa ya yi wannan abune ba dan dole sai yaci zabe ko bai ci ba ya yi ne tsakaninsa da Allah.Kuma Allah  ya gani ya biya musu bukatarsu.Zai kuma  cigaba da yi da yardar Allah

Yarima ya ce duk da cewa ya sami hamayya mai karfi a takararsa ta neman dan majalisar tarayya ya san Allah ke bada mulki,shine mai hanawa bai yi tunanin komai ba, dan yasan in Allah ya bashi babu ma hanaw

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *