Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun) ya dakatar da gangamin yakin neman zaben sa a karamar hukumar Bukkuyum domin alhinin rasuwar mutane shidda da suka yi mummunan hatsarin mota Kan hanyar Gummi zuwa Bukkuyum a daren juma’a.

Hakan yana kunshene cikin wata takarda mai dauke da sa hannun,
Zailani Bappa, me bada shawara na Musamman ga Gwamna kan Harkokin yada labarai.

Ya kara da cewa hatsarin ya afku ne bayan sallar Magariba a lokacin da wasu motoci uku suka yi taho mugama da juna inda rahotanni suka ce mutane shida ne suka rasa rayukansu.

Tun da farko Gwamna Matawalle yana nufin kaddamar da gangamin yakin neman zabensa a garin Bukkuyum bayan Sallar Juma’a, amma ya yanke shawarar dakatar da taron don girmama rayukan da suka rasu a Jihar..

Ya ce a maimakon haka sai ya ziyarci mai martaba sarkin Bukuyum Alhaji Mohammad Usman a fadarsa tare da mika ta’aziyya ga iyalai da al’ummar garin Bukkuyum baki daya, ya ce Allah madaukakin sarki haka ya tsara lamarin cikin hikimarsa, kuma hikimar Allah ita ce mafi alherin zabi ga muminai.

Ya ce Kafin gwamna matawalle ya tashi daga fadar Mai martaba ya umurci tsohon mataimakin gwamnan jihar, Malam Ibrahim Wakkala Liman domin yin addu’a ta musamman ga marigayin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *