Daga Abubakar M Taheer.

Wasu Bata Garin fulani sun Kai Hari ga manoma a Kauyen Takazza dake Karamar Hukumar Guri a Jihar Jigawa.

Cikin wata zantawa da Wakilinmu ya yi da Kansilan Kauyen Hashimu Hassan ya bayyana cewa fulanin sun Fara shirin afka musu tun cikin satin daya gabata da dare.

Bayan sun Sami damar Shiga Garin fulanin sun farmaki manoman Kauyen da misalin karfe 7 da dare inda suka sassara Mutane 13.

Haka Kuma fulanin sun lalata gidaje 23 inda aka garzaya da Wanda suka Sami Raunuka zuwa asibitin Kwanciya ba Malam Aminu Kano.

Dayake magana da mana labarai Shugaban Kungiyar Miyatti Allah Kautal hore Adamu Idris ya bayyana cewa rikicine tsakanin mutanensu da manoma Wanda ake faruwa akai akai a yankin.

Saide kuma a Yau Laraba Jamian tsaro sun bayyana kamawa wasu daga cikin masu laifin tare da kwato dabobi da darajarsu ta Kai naira miliyan ashirin.

Rikicin manoma da fulani na dada daukan sabon salo a Karamar Hukumar ta Guri inda ko a kwanakin baya fulanin sun kashe soja dake bada karya a Garin tare da guduwa da bindigarsa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *