By Bello Hamza, Abuja

A halin yanzu an kammala shirye-shiyen fara aikin samar da cibiyar sarrafa fatu na Naira Miliyan 320 a garin Orogun da ke Jihar Delta, kamar yadda shugaban ma’aikatar NILEST, Farfesa MK Yakubu ya bayyana a tattaunawarsa da manema labarai a ofishinsa da ke Zariya..

Bayani ya nuna cewa, shirin kafa cibiyar yana kunshe ne a cikin kasafin kudin wannan shekarar 2023, za kuma a kafa ne a mazabar majalisar dattawa na Delta ta tsakiya.

Farfesa MK Yakubu ya kara da cewa, irin wannan cibiya ce NILEST ta shirya kafawa a garin Daura ta Jihar Katsina wanda aka ware wa Naira Miliyan 350 da wata kungiya ta yi korafi a kai.

Kungiyar ta nemi ma’aikatar ta dakatar da shirin samar da cibiyar na Daura saboda wai ba a samar da ire-irensa ba a sauran yankunan kasar nan.

Farfesa Yakubu ya yi alkawarin ci gaba gudanar da ayyukansa kamar yadda dokar da ta kafa ma’aikatar ta tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *